Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta gargadi ‘yan kasar nan kan wasu nau’ikan lemo na kuzari masu ɗauke da barasa da hukumomin Ghana suka kama, tare da hana shigo da su, ko sayar da su a Nijeriya.
A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa, ta ce ta samu rahoton cewa Hukumar Abinci da Magunguna ta Ghana ta ƙwace akwatuna kusan 140 na waɗannan kayayyaki a yankin Upper East na ƙasar.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa irin waɗannan abubuwan sha na iya sa masu amfani su kasa gane yadda barasa ta yi musu illa, lamarin da ka iya janyo yawan shan barasa, matsalolin zuciya, rashin daidaiton tunani da motsi, bushewar jiki, matsalar barci da kuma haɗarin afkuwar raunuka ko haɗurra, musamman ga matasa.
NAFDAC ta bukaci masu shigo da kaya, masu rarrabawa, ‘yan kasuwa da masu amfani da su tabbatar ba a shigo da waɗannan kayayyaki ko sayar da su a Nijeriya ba, tare da roƙon jama’a su kai rahoton duk inda suka ga ana sayar da su ko kuma idan sun fuskanci wata illa bayan amfani da su, ga ofishin NAFDAC mafi kusa.
