Hukumar Kula da Ayyukan Ƴansanda ta Ƙasa (PSC) ta amince da korar manyan jami’an ƴansanda uku tare da rage wa wasu 16 muƙamai, sakamakon samun su da laifukan saɓa ƙa’idojin aiki.
Hukumar ta kuma yi wa jami’ai 21 gargaɗi mai tsanani, yayin da wasu biyu suka samu gargaɗi na yau da kullum.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Torty Njoku Kalu, ya fitar ranar Laraba, ya ce an ɗauki matakan ne bayan wani taron hukumar da shugabanta, Hashimu Argungu, ya jagoranta a Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa an wanke jami’ai uku daga zarge-zargen da ake musu, tare da mayar da wasu da aka dakatar bakin aiki.
Hukumar PSC ta jaddada cewa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa, take haƙƙin ɗan Adam da sauran laifukan da ke saɓa ƙa’idojin aikin ƴansanda ba.
