Takardun Babbar Kotun Tarayya da ke Kano sun bayyana sunayen wasu mambobin jam’iyyar NDC uku da suka shigar da ƙarar da ta kai ga hana hukumar INEC wallafa sunan ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo, a sabon jerin ƴan takarar zaɓen 2027.
Mutanen uku su ne Garba Umar Isa, Yau Nasiru da Atiku Jamilu Abubakar, waɗanda suka shigar da ƙarar a ranar 17 ga Oktoba, 2026, suna ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen tsayar da Gwarzo da abokin takararsa, Mustapha Kwankwaso.
Masu ƙarar sun zargi jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da yin tasiri wajen zaɓen Gwarzo da ɗansa Mustapha a matsayin ƴan takarar gwamna da mataimakinsa, ba tare da bin tsarin da ya dace ba.
A ranar 27 ga Oktoba, Mai Shari’a Amobeda ya bayar da umarnin wucin gadi da ya hana INEC wallafa sunayen ƴan takarar NDC ko sauya jerin ƴan takarar gwamnan Kano har sai an saurari ƙarar.
Sai dai kotun ba ta yanke hukuncin ƙarshe kan halaccin takarar Gwarzo ba.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga Nuwamba, bayan lauyan Gwarzo ya nemi kotu ta shigar da shi cikin waɗanda ke da ruwa da tsaki a ƙarar.
