Screenshot
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin sabbin mambobi a Hukumar Wasanni ta Jihar Kano da kuma Kwamitin Gudanarwar Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars, a wani mataki na bunkasa harkokin wasanni da ci gaban matasa a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sanarwar ta ce Alhaji Tukur Babangida shi ne zai jagoranci Hukumar Wasanni ta jihar a matsayin shugaba, yayin da sauran mambobin suka hada da wakilan kungiyoyin kananan hukumomi, cibiyoyin ilimi, masu bukata ta musamman da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni.
Hakazalika, gwamnan ya amince da nadin Alhaji Ahmad Musbahu a matsayin shugaban Kwamitin Gudanarwar Kungiyar Kano Pillars, tare da fitattun mutane da suka hada da Abba Galadima, Sharu Inuwa Rabi’u Ahlan, Fatima Ibrahim Abubakar da tsohon shugaban kungiyar magoya bayan Kano Pillars, Bashir Idris Jide.
Haka kuma, fitaccen dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Ahmed Musa, zai kasance jakadan wasanni a cikin sabon tsarin gudanarwar kungiyar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na bayyana kwarin gwiwarsa akan sabbin shugabannin Hukumar Wasanni da Kano Pillars kan cewar za su samar da sabon yanayi na kwarewa, nasara da ci gaba a harkokin wasanni, tare da mayar da martabar Kano Pillars kamar yadda take a baya.
