Gwamnatin Kano ta bukaci limaman masallatan juma’a da malaman addinin Musulunci da su kara himma wajen wayar da al’umma muhimmancin yin rijista da karbar katin zaben su domin zaben Shugabannin da suka amince da nagartar su.
Kwamshinan yada labaran Kano Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan, a wajen taron bita da karamin kwamitin kar ta kwana kan wayar da kan al’umma rijistar katin zabe ya shiryawa limaman masallatan juma’ar jihar.
Waiya wanda ya samu wakilcin Shugaban karamin kwamitin kwadago kan wayar da kan al’umma Abbas Ibrahim ya ce an shiryawa limaman wayar da kan ne domin su fada kar da al’umma alfanun mallakar katin zabe.
Da yake jawabi a madadin limaman da aka yiwa bitar, Sakataren majalisar malamai ta kasa reshen Kano Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa ya ce yin rijistar zai bawa al’umma damar sauke duk shugaban da basu aminta da jagorancin sa ba, kuma wata hanya ce ta kara samun kaso mai tsokaci daga asusun gwamnatin tarayya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, limaman da suka halarci bitar sun bada tabbacin cewa zasu yi iya bakin kokarin su wajen fahimtar da al’umma muhimmancin yin rijistar la’akari da yadda suke da kusanci da jama’a.
