Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya kafa wani Kwamiti na Musamman wanda zai yi yaki da shan Miyagun kwayoyi da Safarar su, a wani mataki na kara kaimi wajen dakile matsalar da ke addabar matasa da al’ummar jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, inda sanarwar ta ce tsohon Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ne zai jagoranci kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hadar da wakilai daga Hukumar NDLEA, Ma’aikatar lafiya, Hukumar DSS, rundunar ‘yan Sanda, Hukumar NSCDC, Hukumar kwastam, hukumar hana Shige da fice, Hukumar Hisbah, Majalisar Masarautar Kano da kuma Majalisar Malamai, tare da wasu masana da masu ruwa da tsaki.
Sanarwar ta ce an kafa kwamitin ne domin samar da hadin gwiwar hukumomi daban-daban wajen dakile safarar miyagun kwayoyi, gaggauta hukunta masu hannu a harkar da kuma rage yawan masu amfani da kwayoyin ta hanyar fadakarwa da wayar da kai.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa daga cikin ayyukan da aka dorawa kwamitin akwai tattara bayanan sirri, gano da rusa hanyoyin safarar miyagun kwayoyi, gano manyan wuraren da ake rarraba su, da kuma taimakawa hukumomin tsaro wajen gudanar da sumame da kama masu laifi.
