Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai‘Yan sandan Kano sun kama masu kwacen waya 27

‘Yan sandan Kano sun kama masu kwacen waya 27

Date:

Rundunar yan sandan kano ta tabbatar da kama masu kwacen  waya 27 da kuma wasu dake siyan wayar sata.

Wannan na kunshe cikin wani sakon murya da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikewa manema labarai.

Kiyawa yace sun samu wannan nasarar sanadiyar tsarin yansandan cikin alumma wato community policing, inda al’umma ke basu rahotannin maboyar bata gari.

SP Kiyawa ya ce ba za su ragawa dukkan wanda aka kama da laifin kwacce waya, ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana a unguwannin su domin dakile dukkan bata garin da suke aikata barna

Matsalar kwacen waya dai ta dade tana addabar alummar jihar kano, inda alumma da dama suka jikkata harma a wasu Lokutan wasu suka rasa rayukan su.

Latest stories

Related stories