Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHisbah ta ja kunnen ‘yan adadaita sahu kan lika hotunan tsiraici

Hisbah ta ja kunnen ‘yan adadaita sahu kan lika hotunan tsiraici

Date:

Hukumar Hisbah a nan Kano ta ja kunnen direbobin babauran adadaita sahu dake mummunar ta’adar nan ta lika hotunan tsiraici cikin baburansu, wanda tace hakan ya saba da addinin musulinci.

Babban kwamanada hukumar Sheikh Harun Ibn Sina ne ya bayyana haka a ofishinsa yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce hukumar bazata zuba ido ba tana ganin irin wanna dabi’a na faruwa.

Yace sauran da’un da matukan baburan ke yi da suka sabawa addinin musulinci sun hada da kure kida da kuma sa suturar banza duk kuwa da sun san suna daukar matan aure  a baburan nasu.

Daga karshe kwamanada ya gargadi masu irirn wanna hali inda yace idan basu daina ba, to hukumar zata sa kafar wando daya da su.

Latest stories

Related stories