Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn kama dan Najeriya a Saudiya bisa zargin safarar hodar ibilis

An kama dan Najeriya a Saudiya bisa zargin safarar hodar ibilis

Date:

Hukumomin Saudiyya sun kama wani dan Najeriya daya da ’yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a kasar.

Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan kasar ya ce ya samu nasarar dakile yunkurin shigar da hodar iblis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.

’Yan sandan sun ce mutanen hudu sun dade suna aikata laifin safarar hodar ibilis din tare da sayar da ita a cikin kasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.

Jami’an ’yan sandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Safarar kwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekaru masu yawa a gidan yari

 

 

 

Latest stories

Related stories