Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda APC ta raba mukaman shugabancin majalisa ta 10

Yadda APC ta raba mukaman shugabancin majalisa ta 10

Date:

Jam’iyyar APC ta kasa, ta amince da rabon mukamai na shugabancin majalisa ta goma zuwaga shiyyoyi daban-daban.

APC ta ce ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai daga shiyyar Kudu maso Kudu, sai kuma Sanata Barau Jibrin zai kasance mataimakin shugaban majalisar dattijai daga Arewa maso Yamma.

Wata sanarwa da jam’iyyar mai mulki ta fitar, ta ambato kwamitin gudanarwa na APC yana cewa matakin ya zo ne bayan rahotannin tuntuba da tarukan da jam’iyyar ta yi da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Haka zalika jami’iyyar ta APC ta kuma ta ce tana goyon bayan Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalisar ta wakilai daga Arewa maso Yamma.

Sai kuma Ben Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai daga Kudu maso Gabas.

Sai a watan Yuni ne za a kaddamar da sabuwar majalisar, wadda za ta yi aiki kafada da kafada da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu.

Latest stories

Related stories