
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Comrd Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bukaci hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare al’umma bayan hare haren da ’yan bindiga suka kai garuruwan Ƴankamaye a tsanyawa da Lakwaya da ke Karamar Hukumar Gwarzo.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar a ranar Juma’a, 15 ga Mayun, 2026.
Ya ce, tsohon mataimakin Gwamnan ya bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar, inda ya jaddada bukatar daukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sanarwar ta ce, tsohon mataimakin Gwamnan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare haren.
