Ahmad Hamisu Gwale
Babban mai horar da ‘yan wasan Najeriya ‘yan kasa da shekara 20, Flying Eagles, Abdullahi Maikaba, ya gayyaci ‘yan wasa 35 zuwa sansani, ciki har da ‘yan wasan Barau FC, yayin da tawagar ke shirin tunkarar gasar WAFU B U-20.
Matasan kungiyar kwallon kafa ta Barau FC guda biyu sun samu gayyata ne biyo bayan rawar da suka taka a kungiyar a gasar Premier ta Najeriya a bana.
Sa’ad Tijjani wanda dan wasan tsakiya ne kuma dan unguwar Hotoro, kuma yana bugawa kungiyar Barau FC, da ke nan jihar Kano.
Sa’ad, na daya daga cikin ‘yan wasan da suka kafa tarihi na bugawa a gasar, NLO, NNL kuma yanzu zuwa gasar NPFL tare da Barau FC.
Ya gabatar da wasanni na musamman a kungiyar a kakar wasa ta bana kuma a yanzu yana shirin nuna bajinta a matakin kasa tare da tawagar ‘yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya.
Sa’ad ya kuma zura kwallo a raga da taimakawa kungiyar ta Barau a kakar wasa ta bana, inda ya bayyana jajircewarsa da kuma fatan gudunmawar da zai bayar wajen samun nasarar kungiyar.
Sa’ad Tijjani ya fara buga wa Barau FC wasan farkoa gasar NPFL a kakar wasa ta bana, a lokacin da ya zo canji a karawar da suka yi da Rivers United.
A gefe guda kuwa, Adamu Hussain, matashin dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Barau FC, ya fara taka leda a gasar NPFL a kakar wasa ta bana, a wasan da suka buga da Katsina United, kuma ya taka rawar gani a wasu wasanni da dama.
Ya kuma burge magoya bayansa bayan da ya zura kwallo mai kayatarwa a wasan kusa da na karshe na cin kofin shugaban kasa na jihar Kano da kungiyar Chanji FC.
Yanzu dai Adamu yana daya daga cikin ‘yan wasan da su ke taka rawar gani a gasar NPFL a halin yanzu, wanda ke nuna kwazonsa da ci gabansa cikin sauri a kungiyar.
Tuni dai Koci Abdullahi Maikaba ya gayyaci ‘yan wasa 35 zuwa sansanin Flying Eagles yayin da kungiyar ta fara wani sabon salo a karkashin jagorancinsa gabanin gasar WAFU B U-20, da Cote d’Ivoire za ta karbi bakunci a watan Yuli.
Ana sa ran za a fara shirye-shiryen tunkarar gasar yayin da Flying Eagles ke da burin samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na ‘yan kasa da shekaru 20 a badi.
