Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun zargi hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC da take haƙƙinsa na kundin tsarin mulki, inda suka ce an hana shi samun kulawar likita tare da takaita kai masa abinci a wurin da ake tsare da shi.
A wata sanarwa da iyalan suka fitar, sun ce duk da umarnin kotu da ya baiwa El-Rufai damar ganin likitocinsa ba tare da tangarda ba, har yanzu yana tsare a hannun ICPC.
Iyalan sun ce likitansa ya je hedikwatar hukumar domin tattauna sakamakon gwaje-gwajen lafiyarsa, amma jami’an ICPC suka hana shi ganawa da El-Rufai, suna cewa sai an samu rubutacciyar izini daga shugaban hukumar.
Sun kuma yi zargin cewa matar El-Rufai, an hana ta kai masa abincin dare saboda ƙa’idar cikin gida da ta hana karɓar abinci bayan ƙarfe 6:30 na yamma.
Iyalan sun bayyana hakan a matsayin cin zarafi da tauye haƙƙin ɗan Adam, tare da kira ga ICPC da ta mutunta haƙƙoƙin tsohon gwamnan.
Lamarin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bukaci a saki El-Rufai.
