Saurari premier Radio
41.7 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTsohon gwamnan Katsina Ibrahim Shema ya nemi PDP ta janye dakatarwar da...

Tsohon gwamnan Katsina Ibrahim Shema ya nemi PDP ta janye dakatarwar da tayi masa ko ya fice daga jam’iyar cikin awanni 48

Date:

Tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema, ya nemi kwamitin gudanarwar jam’iyar PDP da ya janye dakatarwar da yayi masa da wasu mambobin jam’iyar cikin awanni 48.

Shema, ya kuma nemi jam’iyar data janye rushe shugabanin jam’iyar na jihar Katsina da tayi.

Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis ne PDP ta sanar da dakatar da wasu daga cikin mambobin jam’iyar ciki harda Shema bisa zargin yiwa jam’iyar zagon kasa.

Cikin takardar da Shema ya aikewa shugaban jam’iyar na kasa Iyorchia Ayu, a Juma’ar nan ya nemi jam’iyar ta PDP data janye dakatarwar cikin awanni 48 ko ya fice daga cikin jam’iyar.

APC ta shirya lauyoyinta domin tunkarar PDP da LP a kotu

Tsohon gwamnan na Katsina ya kara da cewa kwamitin gudanarwar jam’iyar baiyi biyayya ga sashi na 56 (6) da (7) da kuma sashi na 59 (3) na kundin tsarin mulkin jam’iyar da ya bada damar jin bagaren wadanda ake zargi kafin dakatar da su.

Shima tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim cikin wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar nan yayi watsi da matakin dakatar dashi da jam’iyar tayi.

Rikici dai ya balle a jam’iyar PDP tun bayan rashin nasara da tayi a zaben shugaban kasa da aka kammala wanda ta kai ga ta dakatar da wasu daga cikin ‘ya’yan ta saboda zargi yiwa jam’iyar zagon kasa.

Latest stories

Related stories