Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAPC ta shirya lauyoyinta domin tunkarar PDP da LP a kotu

APC ta shirya lauyoyinta domin tunkarar PDP da LP a kotu

Date:

Jam’iyyar APC

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ce jam’iyyar ta shirya lauyoyinta tsaf domin tunkarar lauyoyin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da LP a kotu.

A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar da Peter Obi suka kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata suna cewa za su kai kotu, wanda ɗan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a cikinsa , kuma INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe shi.

Da yake tattunawa da manema labarai daraktan hulda da jama’a kuma kakakin kwamitin Festus Keyamo yace jam’iyyar ta tanadi tawagar manyan lauyoyi na Najeriya wanda suke a shirye domin kare nasarar da Tinubu ya samu lokacin da za su kotu da Atiku da Obi.

Ya ce “tuni mun hada tawagarmu ta lauyoyi. Muna da wadanda su kuma suka zo a radin kansu wanda dukkansu za su yi aikin kariyar.”

Latest stories

Related stories