Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZa mu kama wasu gwamnoni ranar 29 ga Mayu-EFCC

Za mu kama wasu gwamnoni ranar 29 ga Mayu-EFCC

Date:

Hukumar EFCC ta ce ta za ta kama wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke karewa da ake zargi da ayyukan rashawa, bayan miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da Jaridar Daily Trust. 

Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan waɗanda suke shirin kamawa ba da zarar sun sauka daga mulki.

A Najeriya dai, gwamnoni na cikin jami’an gwamnati da ke da kariya wadda ya hana a a kama su idan suna kan mulki.

Shugaban na EFCC ya ce akwai ma’aikatun gwmanati guda biyu da hukumar ke bincike a kansu a halin yanzu saboda ayyuka da suka saɓa wa ka’ida da suke yi.

A cewarsa, a ɗaya daga cikin ma’aikatun an yi almundahanar kuɗaɗe ta N4bn na wasu kwangiloli kusan 20.,

“A yanzu haka, muna binciken ma’aikatu biyu da aka biya kuɗaɗen har sau biyu a cikinsu.

“Waɗannan kwangiloli ne da aka yi tun shekarar 2018, sannan wasu mutane masu karfin hali suka fito da suka bayyana batun.

Ya ce an buga takardun bogi a cikin ma’aikatun, sannan da haɗin-bakin wasu ma’aikata, aka kirkiri takardun karya tare da biyan kuɗi.

Bawa ya ce muddin aka mayar da harkoin gwamnati ta hanyar zamani, ba za a samu irin waɗannan badaƙaloli ba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...