Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda huɗu da ake tare da ƙwato makamai da kayan aiki a lokacin wani samame da suka kai a yankin dajin Sambisa da ke jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce, an gudanar da aikin ne a safiyar ranar 30 ga Afrilu, ta karkashin dakarun rundunar sojojin musamman ta 21 tare da haɗin gwiwar dakarun sa kai na yankin.
Majiyoyin sun bayyana cewa, sojojin sun yi sansani zuwa wani wurin da ake zargin ’yan ta’adda ne bayanan sirri kan motsin ’yan ta’addan da suka samu.
A lokacin da ake wannan batakashin, an kashe ’yan ta’adda huɗu, yayin da sojoji suka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da harsasai 12.
Sauran kayayyakin da aka gano sun haɗa da buhu biyu na masara da aka niƙa da fakitin taliya, wanda ake kyautata zaton wani ɓangare ne na kayan abincin ’yan ta’addan.
Daga bisani Sojojin Operation Hadin Kai ta dawo sansaninsu lafiya ba tare da jin wani rauni ba, yayin da ake ci gaba da aikin sa ido da share fagen daga a yankin.
