Tsohuwar ‘yar takarar gwamnan Jihar Adamawa a shekarar 2023, Sanata Aishatu Dahiru Binani, ta fice daga jam’iyyar ADC tare da komawa jam’iyyar NDC.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Sanata Aisha Binani ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne bayan nazari kan tsarin jam’iyyar NDC, inda ta ce ta gamsu da yadda take mayar da hankali kan shugabanci mai tsari da kuma manufofi masu kyau.
Ta kuma jaddada cewa shawarar komawar ta samo asali ne daga magoya bayanta, wadanda tuni suka fara shiga jam’iyyar NDC kafin ta shiga cikin jami’iyyar.
Da yake nasa jawabin jim kadan bayan karbar Sanata Aisha Dahiru Binani cikin jami’iyyar, shugaban NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya bada tabbacin marawa Sanata Aisha Binani baya domin samun nasara.
Ana sa ran wannan sauyin jam’iyya zai sauya tsarin siyasa a Jihar Adamawa gabanin zaben 2027.
A shekarar 2023 Sanata Aisha Binani ta tsaya takarar gwamnan jihar Adamawa, inda aka samu cece-kuce bayan an ayyana ta a matsayin wadda ta yi nasara kafin daga bisani hukumar INEC ta soke sakamakon.
