Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Tuesday, May 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaba Bola Tinubu yace ba ya fargaba kan hukuncin da kotun sauraren...

Shugaba Bola Tinubu yace ba ya fargaba kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe za ta yanke a gobe Laraba.

Date:

Shugaba Bola Tinubu yace ba ya fargaba kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben kasar nan za ta yanke domin yana da yakini shi ya yi nasara a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV ranar Litinin da maraice.
An zaben, INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 37 na kuri’un da aka kada.
Dan takarar da ke biye masa shi ne Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kashi 29 yayin da dan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi ya samu kashi 25.
Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu ‘yan takarar sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.
A gobe Laraba ake sa ran kotun za ta yanke hukunci game da zaben a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya yi balaguro zuwa India domin halartar taron kungiyar kasashen G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya.

Latest stories

Related stories