Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar Kwadago ta kasa NLC ta fara yajin aiki a fadin kasar...

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta fara yajin aiki a fadin kasar nan a yau Talata, saboda tsadar rayuwar da al’umma suke fama da ita sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi.

Date:

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta fara yajin aiki a fadin kasar nan a yau Talata, saboda tsadar rayuwar da al’umma suke fama da ita sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi.
NLC ta fara yajin aiki gargadin na kwana biyu ne washegarin da ta kaurace wa zaman sulhun da gwamnatin ta gayyace ta da nufin ganin kungiyar ta hakura.
Yajin aikin na zuwa ne kwanaki 99 bayan Shugaba Bola Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo karshen tallafin a yayin jawabinsa na fara aiki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Hakan ya haddasa ninkuwar farashin litar man daga N197 zuwa 620, wanda kuma ya yi sanadin hauhawar farashin kayan masarufi da na sufuri da sauran bangarorin rayuwa.
Tun a lokacin da Tinubu ya sanar da karshen tallafin kungiyar NLC ta yi watsi da matakin a matsayin riga-mallam-masallaci, bisa hujjar cewa gwamnati ba ta yi tanadin abubuwan da ya kamata na rage tasirin janye tallafin ba da farko.
Kwanaki 40 da suka gabata, a ranar 26 ga watan Yuni, kungiyar ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, da nufin shiga yajin aiki bayan hakan.

Latest stories

Related stories