Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi cikin aminci ba za ta dawo ba har sai kasashen yamma sun biya bukatun Moscow na saukaka fitar da kayayyakin noma daga Rasha.
Putin ya bayyana hakan ne bayan tattaunawa da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a birnin Sochi na kasar Rasha.
A taron manema labarai na hadin gwiwa da shugabannin biyu suka gudanar, Vladimir Putin ya ce Rasha na gab da kulla yarjejeniyar da za ta ba ta damar samar da hatsi kyauta ga kasashen Afirka shida.
Kasashen da suka hada da Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Eritrea da Mali da Somalia da kuma Zimbabwe kowaccen su za ta samu tan dubu 50 na hatsi kyauta, inda Rasha za ta dauki nauyin tura musu shi kasashen su.
Da yake magana a watan Yuli lokacin da aka fara sanar da kudirin, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kira yarjejeniyar a matsayin tallafi ga yan gudun hijirar wasu kasashe, yana mai fatan cewa ba zai kasance sila ga matakin da Rasha ta yi na ficewa daga yarjejeniyar ba
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi cikin aminci ba za ta dawo ba har sai kasashen yamma sun biya bukatunta.
Date: