Mukhtar Yahya Usman
Hukumar DSS ta ja kunnen masu yin kalaman rashin ‘kan gado’ game da kama Tukur Mamu mai shiga tsakanin ‘yan ta’adda da gwamnati.
Hukumar ta ce sakamakon binciken da take gabatarwa abune mai rikitarwa da zai bada mamaki.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Peter Afunanya ne ya bayyana haka a Abuja ranar Lahadi.
Ya ce gargadin ya zama dole la’akari da yadda wasu ke yada kalaman batanci ga hukumar tun bayan kama Mamu a shafukansu na sada zumunta.
A cewar hukumar ba za ta rudu da labaran da wasu jaridu da shafukan sada zumunta ke wallafawa ba da zai dauke mata hankali.
Ya ce akwai bukatar a barsu suyi bincike cikin nutsuwa, wanda sakamakonsa abune mai matukar razanarwa.
“A halin yanzu, Hukumar za ta daina tsokaci kan batun har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukunci,” in ji shi.
Jamian tsaro na Kasa da Kasa ne dai suka kama Tukur Mamu afilin jirgin saman Alkahira na kasar Masar.