Mukhtar Yahya Usman
Rundunar ’Yan Sandan Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a hadarin kwalekwale da ya auku a Karamar Hukumar Ringim.
Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan a Dutse babba birnin jihar.
Ya ce kwale-kwalen na dauke ne da fasinjoji 13 a hanyarsu ta zuwa ta’aziya.
“Da karfe 12:40 na ranar Lahadi ne muka samu labarin wani kwalekwale dauke da mutane 13 da ya taso daga kauyen Dabi zuwa Siyangu da ke karamar hukumar Ringim ya kife.
“Kuma alamu na nuna karon da jirgin ya yi da wani abu ne ya haddasa hatsarin,” in ji shi.
Kakakin ya ce da samun labarin, ’yan sandan suka garzaya zuwa kogin da taimakon masuntan da ke wurin domin ceto fasinjojin.
“Mun ceto mutane bakwai, kuma mun garzaya da su asibiti domin ba su agajain gaggawa.
“Sai dai biyu daga ciki wato Lubabatu Garba mai shekara 30 da kuma Mahmud Surajo mai shekara uku sun rasu.”
Shiisu ya ce sauran mutane biyar din na kwance a asibiti suna karbar magani, yayin da wadanda suka rasu kuma aka mika su ga iyalinsu domin binne su.
“Sauran mutane shidan kuma har yanzu ba mu gano su ba, amma muna ci gaba da lalube,” in ji shi.
Idan ba a manta ba dai ko a makon da ya gabata sai da aka samu wasu mata uku da jaririya da suka nutse a kogi, sakamkon hadarin kwalekwale a Karamar Hukumar Guri ta Jihar.