Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda 'yar shekara 13 ta haddace kur'ani da rubutashi a Katsina

Yadda ‘yar shekara 13 ta haddace kur’ani da rubutashi a Katsina

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wata yarinya ‘yar shekara 13 Zuwaira Ahmad dake ƙauyen Kagara a ƙaramar hukumar Kafur a jihar Katsina ta haddace Alƙur’ani Mai Girma tare da rubuta shi.

 

Da yake jawabi a wani taro da aka shirya don girmama yarinyar, Dagacin Mahuta, Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ci gaba.

 

Ya ce wannan babban ci gaba ne da aka samu a ƙauyen da ma jihar gaba ɗaya ta fannin ilimin addinin Musulunci.

 

Bello ya yaba wa iyaye, malamai da sauran jama’a a yankin bisa tabbatar da kyakkyawar tarbiyya ga ‘ya’yansu, yana mai kira a gare su da ci gaba da haka.

 

Dagacin, wanda kuma shi ne Danejin Katsina, ya tabbatar wa sarakunan gargajiya goyon bayansa ga ci gaban ilimin addinin Musulunci.

 

A nasa bangaren shugaban ƙaramar hukumar Ƙafur, Garba Kanya, ya nuna jin daɗinsa bisa hazaƙar ɗalibar, kuma ya ce za a ɗauki nauyin karatunta daga sakandare har jami’a.

 

Shugaban makarantar da Zuwaira ta yi karatu, Sheikh Sani Kagara, ya ce an kafa makarantar ne don bayar da ingantaccen ilimin addinin Musulunci a tsakanin yara a yankin.

 

A cewarsa, yarinyar ta haddace Alƙur’anin ne a cikin shekara huɗu, ya kuma danganta wannan nasara ga iyaye da jajircewar malaman makarantar.

 

A jawabinsa, mahaifin Zuwaira, Ahmad Sani, ya yi godiya bisa goyon bayan da aka ba shi shi da ‘yarsa, yana mai kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su samu ilimin addini da na Boko.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...