Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAl'ummar Rurum, Tiga na bukatar daukin gaggawa- Kabiru Alhassan Rurum

Al’ummar Rurum, Tiga na bukatar daukin gaggawa- Kabiru Alhassan Rurum

Date:

Shehu Usman Salihu

Ɗan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure Kabiru Alhassan Rurum ya roki gwamnati ta gaggauta kai dauki ga al’ummar Tiga da Rurum bisa fargabar fashewa Dam din Tiga.

 

Wanann na zuwa ne bayan da Dan Majalisar ya Kai ziyarar gani da Ido ga bakin ruwan da ya fara ambaliyar a jiya Asabar.

 

A cewarsa ana zargin an samu ambaliyar ne sakamakon rufe wasu madatsun ruwa da hukumar a Hadejia Jama’are ta yi.

 

“Ruwan ya karya madatsar babbar gadar da ta hada garin Rurum da Tiga Kuma ya sake fasa kwalta mai
mita 25 daga gadar, nan ma ya yiwa kansa hanya”.

 

“Ruwan na gudu cikin matsanancin karfin da duk abinda ya tarar zaiyi awon gaba dashi Kuma tuni ya shafe daruruwan gonaki baya ga wasu kauyuka da ya tasa”

 

Haka kuma Rurum ya bukaci mutanen dake garuruwan dake kusa da Dam din su gaggauta barin wuraren.

 

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta tarayya su kaiwa al’umma dauki dan daukar matakin da ya dace.

 

Rurum ya jajantawa manoma da al’ummar garuruwan da abin ya shafa tare da tabbatar musu kokarin sa na ganin an kai musu dauki.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...