Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar Yan Sandan Kano Ta Kalubalanci Bayar Da Belin Alasan Ado Doguwa.

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kalubalanci Bayar Da Belin Alasan Ado Doguwa.

Date:

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kalubalanci bayar da belin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa daga gidan yari da wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yi.

Lauyan yan sanda, Barista AD Saleh, ya nuna damuwa kan hakan jiya Laraba a zaman sauraron karar da shugaban masu rinjayen ya shigar.

Ya bukaci mai shari’a, Muhammad Yunusa, da ya yi watsi da bukatar da Doguwa da ya shigar na neman hana jami’an tsaro kama shi, cin zarafin shi ko tursasa yin wani abu har sai an gurfanar da shi a gaban kuliya.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Maris, mai shari’a Yunusa ya bayar da balin Doguwa daga gidan yari bayan wata kotun majistare ta bayar da umarnin tsare shi.

Ana yiwa doguwa tuhume-tuhume biyar da suka hada da kisan kai, hada baki, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, da tada zaune tsaye da hargitsa jama’a.

Mai shari’a Yunusa ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga Mayu, domin yanke hukunci kan bukatar Rundunar yan sandan jihar Kano.

Latest stories

Related stories