Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai  Ana Zargin Likita Da Yi Wa Mara Lafiya Fyade A Asibiti.

  Ana Zargin Likita Da Yi Wa Mara Lafiya Fyade A Asibiti.

Date:

Rundunar yan sandan jihar Kwara, ta gurfanar da shugaban wani asibitin da ke Ilori, Dokta Ayodele, a gaban wata kotun majistare kan zargin yi wa wata mara lafiya fyade.

Rundunar ta bayyana wa kotu cewa, likitan ya yi wa mara lafiyar, wadda kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce, allurar kashe kuzari, lokacin da ta je duba lafiyarta, sannan ya yi mata fyade.

Dan sanda mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, ya fadawa kotun cewa likitan, wanda ya shekara 27 yana aiki, ya aikata laifukan fyade da kuma rashin dattaku, don haka ya kamata a hukunta shi.

Takardar tuhuma da aka gabatar wa kotun, ta nuna cewa yayin bincike an gano bidiyon fyaden da likitan ya yi, sannan gwajin asibiti ya tabbatar yin fyaden.

Bayan sauraren kofare-korafen, alkalin kotun, Gbadeyan Jumoke Kamson, ya amince da tsare likitan tare da dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...