Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDaliban da suka biya kudin Makaranta ne kawai za su rubuta jarrabawa-KSP

Daliban da suka biya kudin Makaranta ne kawai za su rubuta jarrabawa-KSP

Date:

Kwalejin kimiyya ta Jihar Kano ta ayyana ranar 14 ga Mayun da muke ciki, a matsayin ranar da zata rufe damar biyan kudin Makaranta da daliban wannan shekarar su keyi.

Shugaban Kwalejin Farfesa Kabiru Bello Dungurawa ne ya bayyana hakan a wani taron manema Labarai da ya gudanar a ranar Laraba.

Kafin fitar da sanarwar hakan, dai sai da masu ruwa da tsaki na Kwalejin suka gudanar da taron da suka saba gudanarwa duk wata domin duba kan yadda kwalejin ke ciki.

Wanda kuma cikin mahimman abubawan da suka tattauna harda batun shirye-shiryen da Kwalejin keyi na tinkarar fara rubuta jarrababawar zangon farko ta wannan shekarar.

Dunguruwa ya ce daukar matakin na da alaka da yadda Kwalejin ta baiwa daliban dama ta akalla wata biyar domin su samu damar biyan kudin Makaranta.

Ya kara da cewa tuni Kwalejin ta sanya ranar 15 ga watan da muke na Mayu, ciki domin fara rubutawa jarrababawar zangon farko ta wannan shekarar.

Yana Mai shawartar dalibai da su gaggauta biyan kudin Makaranta a kwanakin da suka rage, da rashin hakan zai sanya dalibi gaza damar rubuta jarrabawar.

To sai dai wannan matakin na rufe waadin biyan kudin Makaranta na 14 ga watan Mayu, bai shafi daliban da suke karatun Part-time ba.

Harma Farfesa Kabiru Bello Dungurawa ya ce gaba kadan Kwalejin zata sanar da ranar rufe biyan kudin daliban da suke karatun Part time.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...