Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai‘Mu, Y’an siyasa mun cuci nijeriya’ - Amb. Kazaure

‘Mu, Y’an siyasa mun cuci nijeriya’ – Amb. Kazaure

Date:

Tsohon ministan ayyuka na kasar nan ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya ayyana kansa cikin wadanda ya kamata a daure bisa yin wadaka da dukiyar al’umma.

Ya bayyana hakane yayin hirar sa da sashin hausa na gidan Radiyon Faransa a ranar Alhamis.

Ya ce dukkan ‘yan siyasar kasar nan daya suke kuma babu talaka a zuciyar su ko kadan.

Ibrahim Musa Kazaure wanda tsohon ambasadan kasar nan ne a Saudia ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kama ‘yan siyasar kasar nan da suka saci dukiyar al’umma ciki kuwa harda shi kansa.

Dangane da batun tattalin arziki kuwa Ibrahim Kazaure ya ce babu wani abu da dan Najeriya da ya rike mukamin gwamnati ya tsinana tun daga shekarar 1999 da aka dawo mulkin dimukuradiya.

Sai bayan na zama shugaban kasa sannan matasa za su karba-Tinibu
“Koni da nake magana dakai yanzu abun da mukayiwa kasar nan mun cancanci a daure mu”,

“Ina fada ni Ibrahim Musa Kazaure mun cuci Najeriya da talakawanta”,

” Gaskiya itace abinda mukayi a lokacin mu
bashi ya kamata muyi ba, saboda wasun mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba,” a cewar sa.

Yajin aikin ASUU: Dalibai na zanga-zanga a Kano
A cewar sa ” a kasar nan ne kawai bangaren ilimi yake cikin halin ha’ula’I kuma malamai ke tafiya yajin aiki koda yaushe.

“To yaushe ne zamu cigaba? Ba zan nemi wata kujera a kasar nan ba koda kuwa zasu bani kyauta, ba zanyi ba.

” Na kalubalanci kowa a kasar nan harda shugaban kasa, kaje ka duba. Na fadi gaskiya. Duk wanda ya saci kudin kasar nan ya dawo dashi.

 2013:Yahya Bello ne ya cancanci zama shugaban kasa-Rescue Nigeria Mission

Na fadawa shugaban kasa Buhari cewa duk wanda yayi sata a kamashi ciki kuwa har dani, zamu dawo da ita idan an tabbatar,” a cewar Ambasada Ibrahim Musa Kazaure.

Latest stories

Related stories