Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Saturday, February 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSiyasar Kano:Mua'z Magaji ya fice daga APC

Siyasar Kano:Mua’z Magaji ya fice daga APC

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya ya fice daga jam’iyyar APC.
Dansarauniya ya kuma bukaci dukkan jam’iyyun siyasa da su shaida cewar daga ranar Asabar 12 ga watan Maris ɗin shekarar 2023 ya bar jam’iyyar.

Ɗan Sarauniya wanda shi ne jagoran rundunar siyasar Win-Win, kuma mamba a tafiyar G7 da ke biyayya ga tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da hakan ne a shafinsa na facebook a safiyar yau Asabar.

Haka kuma Mu’azu Magaji, ya daɗe yana sukar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, wanda hakance ta sanya ya fuskanci shari’a tsakaninsa da gwamnatin Kano bisa zargin ɓatawa Gwamna suna.

A jiya juma’a dai tsohon kwamishinan ya wallafa hotunan wata ziyara da ya kaiwa Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda jigo ne a jam’iyyar ta PDP.

Ficewar Mu’az Magaji ɗin dai na zuwa kwanaki biyu da wasu daga cikin jiga – jiga-jigai a jam’iyyar PDP Kwankwasiyya su ka nuna ba za su bi Madugun Kwankwasiyyar zuwa sabuwar NNPP da ya ke shirin komawa nan da karshen watan Maris ba.

Latest stories

Related stories