Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAkwai yiwuwar na koma PDP-Mua'azu Magaji

Akwai yiwuwar na koma PDP-Mua’azu Magaji

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Tsohon Kwamishinan Ganduje Mu’azu Magaji Dan Sarauniya ya ce  akwai yiwuwar ya koma jam’iyyar PDP jim kadan bayan ficewarsa daga APC.

A zantawarsa da Premier Radio Dan Sarauniya ya ce yana nan yana tuntubar wadanda suka da ce kan jam’iyyar da ya kamata ya koma.

Ya ce a jiya sun kaiwa Bello Hayatu Gwarozo jigo a jam’iyyar PDPn Kano ziyara inda suka tattauna kan batutuwa da dama.

Da sanyin safiyar yau Asabar ne Dan Sarauniya ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a shafin sa ma Facebook.

Babu ragowar mai hankali a APC banda Buhari

Ya ce ya fice daga jam’iyyar  ne don babu wani mai hankali da ya rage a cikinta banda Muhammadu Buhari.

Dan sarauniya ya ce a yanzu halin da jam’iyyar APC ta fada na rashin kan gado shi ne zai kai ga karasa wargazata.

Ya kara da cewa ba za su zauna cikin jam’iyyar ba suna ganin abubuwa na tafiya ba dai-daiba kuma ba za su iya gyarawaba.

A don hakan ne ya zabi ficewa daga jam’iyyar domin komawa inda zai tallafawa jama’a da irin rawr da zai iya takawa.

“In Kaduba irin yanayin da talaka ke ciki da halin da kasar ke ciki duka ba a cimma burin canjin da ake ta kara ba, sai ma ta’azzarar rayuwa da aka samu.

“Idan kazo jihohin mu misali jihar Kano za ka tarar da siyasa ta lalalce, tsarin gwamnati ya kara tabarbarwa.

“Dole mu da muke burin kowo wannan canjin mu sake tunani, idan ka cire Muhammadu Buhari kuma a APC, to an shiga hauma-hauma, Sankai da sarar juna, jam’iyyar APC sai abinda Allah ya yi.

“A kan wannan gabar muka ga ya kamata a ce mu fice daga wanann jam’iyya.

Ba tsoron Ganduje ne ya sana fitaba

Mua’azu Magaji ya kara da cewa kamashi da gwamantin Kano ta sa aka yi aka daure bashi da alaka da ficewarsa daga Jam’iyyar.

Ya ce da yanason zama tare da gwanmanti da lokacin da aka bashi Kwamishina a jam’iyyar ta APC sai ya ja bakinsa ya yi shiru.

Ya ce batun kishin al’umma da kuma neman kawo canji mai dorewa ne ya sanyashi ficewa daga jam’iyyar.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories