Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikin APC: Buhari ya yi gargadi mai zafi

Rikin APC: Buhari ya yi gargadi mai zafi

Date:

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi gargaɗi ga shugabanni da ƴan jam’iyar APC da su daina nuna wa juna yatsa da sa-in-sa a junansu, yayin da jam’iyar ke tunkarar babban taron ta na ƙasa a ranar 26 ga watan Maris.

APC dai ta sake nutsa wa cikin rikici bayan da gwamnoni 19, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai su ka hamɓarar da kujerar shugaban kwamitin riƙo na jam’iyar, Gwamna Mai Mala Buni.

Ana dai indai zargin da umarnin shugaban ƙasa su ka aikata hakan.

Muhammadu Buhari ya ja kunnen ƴan jam’iyar da su ci gaba da jajirce wa da haɗa kai domin jam’iyar ta ci gaba da tafiya a kan gwadabenta na nasara da ta ke kai.

Ya kuma buga misali da jam’iyar adawa ta PDP, inda ya ce duk karfin ta a ƙasar nan amma yanzu ta yi ƙasa.

A sanarwar da kakakin sa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce APC ta kwashe kusan shekaru 8 tana mamaye sauran jam’iyyu sabo da ta buɗe kofar ta ga duk wanda yanke so ya shigo da ga wata jam’iya, babba ko karama.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...