Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabu gamsasshiyar sheda kan zargin hannun DCP Abba Kyari a badakalar Hushpuppi:Malami.

Babu gamsasshiyar sheda kan zargin hannun DCP Abba Kyari a badakalar Hushpuppi:Malami.

Date:

Muhammad Bello Dabai

Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN) yace shedun da aka gabatar kan zargin DCP Abba Kyari na cuwa cuwar kudi tare da sanannen dan damfarar nan Hushpuppi, basu da inganci.

A watan Janairun da ya gabata ne, Malami ya tabbatar da cewa binciken yan sanda ya gano Kyari na da hannu a badakalar, tare da umartar tuhumarsa akai, da kuma wasu laifuka 33.

To sai dai a wasikar da ya aikewa babban sifetan yan sanda na kasa, mai kwanan watan 4 ga Fabarairun 2022, ya umarci a sake binciken.

Yace shedun dake kunshe cikin kundin tuhumar “Basu gamsar wajen tabbatar da hannun Kyari a badakalar naira 279m ba”.

Malami yace hukumar yan sanda nada zarafin ladabtar da Kyarin, bisa saba dokokin aiki wajen kulla alaka da masu kashi a gindi, a matsayinsa na babban jami’in dan sanda.

Ya kuma ce za’a iya hukunta Kyari da laifin saba dokar hukumar yan sanda ta shafukan sada zumunta, kan yiwa cibiyar binciken Amurka FBI martani a shafin Facebook, da kuma tsare wani Vincent Chibuzor na tsawon sama da wata guda, ba tare da umarnin kotu ba.

Tuni labarin ya janyo cece kuce a shafukan sada zumunta, inda wadansu ke zargin malami da kokarin ceto Kyari, ta hanyar wanke shi daga laifi.

A sanarwar da kakakinsa, Dr Umaru Gwandu ya fitar a yau, yace anyiwa wasikar Malami fahimtar baibai.

“Matsayar ofishin ministan shari’a itace, babu gamsassun shedun dake nuna hannun Kyari a badakalar kudi.”

“An tayar da wannan batu ne domin jan hankali kan a zurfafa bincike, ta yadda za’a kai ga matakin gaskiya”.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories