33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBan wanke DCP Abba Kyari ba-Malami

Ban wanke DCP Abba Kyari ba-Malami

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Muhammad Bello Dabai

Ministan shari’a na kasa Abubakar Malami ya ce ko kadan ofishinsa bai wanke Abba Kyari daga zarge zargen da ake yi masa ba.
Ya ce kafafen yada Labarai ne kawai suka canja masa kalamai.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in yada labaransa Dr Umar Gwandu ya fitar da yammacin yau Lahadi.
Dr Gwandu ya ce ga alama jama’a basu fahimci kalamansa na baya ba, wanda yace jarida suka yadawa jama’a ba dai-dai ba.

Ya ce ofishin attorney janar din ya bayar da dama ne da a kara tsananta bincike kan wasu zarge zargen da ake yiwa Abba Kyarin.

Gwandu ya ce har yanzu ofinshin attorney janar bai yanke wata matsaya akan matsalar ba, duk da cewa ba a samu wata hujja mai gamsarwa kan rahoton farko da ya fito ba.

Latest stories