37.6 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabarai 2013:Yahya Bello ne ya cancanci zama shugaban kasa-Rescue Nigeria Mission

 2013:Yahya Bello ne ya cancanci zama shugaban kasa-Rescue Nigeria Mission

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar  Yahya Usman

Kungiyar Rescue Nigeria Mission ta ce babu wanda ya cancanta da ya shugabanci kasar nan a kakar zabe mai zuwa kamar gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello.

Jami’in Kunigiyar a nan Kano Abdul Amata Maikwashewa ne ya bayyana hakan ya yin taron jin ra’ayoyin jama’a tsakanin matasa ranar Asabar a nan Kano.

Mai kwashewa ya ce Yahya Bello ya taka rawa ainun ga rayuwar matasa a kasar nan, musamman jawosu jikin gwamnati tare da samar musu da damarmaki.

Ya ce wanan kungiya ta yi nufi marawa Yahya Bello baya ne ganin cewa har yanzu babu wani mai nagartarsa cikin wadanda ke nema takarar shugabancin kasar nan.

“Mun yanke shawarar musameshi, mu rokeshi Allah da Annabi ya fito takarar shugabancin kasar nan, saboda baya cikin layin tsofaffi, matashi ne kamarmu wanda yake fahintar menene bukatun samari da kuma jansu a jiki wajen gudanar da mulki a kasar nan.

A nasa jawabin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kogi Abdulkareem Jamilu ya ce yan  kasar nan ya kamata su shaki iskakar Mulki mai dadi su kuma marawa wanda zai ciyar da su gaba baya.

A don hakan ne ya bukaci matasa a kasar nan da kada su yarda wasu tsoffin yan siyasa ko wadanda basu cancantaba su dinga juya akalarsu, musamman ma da matasan suke da koso 70 cikin jama’ar kasar nan.

Ya kuma godewa wadanda suka shirya taron, bisa karfin gwiwar da suke da shi kan Yahya Bello, inda ya ce gwamnan na da duk wata dama da iko da zai magance matsalolin kasar nan.

Latest stories