Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC: Tsagin Shekarau ya yi watsi da shirin sulhun uwar jam'iyya

Rikicin APC: Tsagin Shekarau ya yi watsi da shirin sulhun uwar jam’iyya

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Kano na ƙara daukar sabon salo bayan ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da sanarwar uwar jam’iyya kan sulhunta rikicin ‘ya’yanta.

Matsayar tsagin Sanata Shekarau da ya zabi Alhaji Haruna Dan-Zago a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano na da alaƙa da bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje jagorancin kwamitin da zai warware matsalar.

Wata sanarwa da ta fito daga uwar jasm’iyyar ta kas adage nuna bagaren ganduje ya jagoranci tsara sulhun, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba.

”Matsayinmu akan wannan sanarwa matakai ne kamar guda uku: a duk zaman da muka yi kamar sau biyu ko sau uku, wanda mai girma gwamna Ganduje ya na wurin da mukarrabansa da wadanda muma muka je tare da su, karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar gwamnan jihar Yobe Maimala Buni.

“An nemi kowanne bangare ya bayyana matsayarsa da abin da suke son ayi da shawarar waraka kan wannan matsala, dukka mun bayar da na mu. Shugaban jam’iyya ya ce za su koma su kalli bayanan da dukka muka yi domin fito da wata matsaya, da shawarar abin da ya dace a yi.”

Sanata Shekarau ya kara da cewa, sanarwar da jam’iyyar APC ta fitar ba ta yi magana akan matsayar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu ba, sannan jam’iyya ba ta fadi komai tsakanin abin da bangarorin biyu suka bukata ba.

Abu na biyu kafin a kawo takardar a matsayin wanda ya ke jagorantar ɗaya bangaren, sai da aka kai wa gwamna Ganduje takardar wadda kamata ya yi ta zama tsakanin shugaban jam’iyyar, ko hedikwatar jam’iyya, da Gwamna da kuma ni shugaban ɗayan barin jam’iyyar, in ji Shekarau

Sannan ya ci gaba da cewa kafin su samu takardar ta shiga duniya tana yawo a shafukan sada zumunta.

“Yaran gwamna na cewa an dankawa gwamna jam’iyya ai ta koma hannunsa da maganganu makamantan haka.

“Abu na uku shi ne ya ya mutane biyu su na jayayya, sai kuma a ce ɗaya daga cikin wadanda ake jayayya da shi ne zai jagoranci sasantawar, alhalin shi ya jagoranci waccan sasantawar da ba a yi mana adalci ba, da muke ganin an zalunce mu, ta ya ya za a yi mana adalci a yanzu.”

Kamata ya yi uwar jam’iyya ta wakilta wanda zai jagoranci wannan zama. Don haka ba mu amince da shi ba, mun yi fatali da shi, ba mu yadda ba, ba kuma za mu amince ba, a karshen takardarmu mun fadawa uwar jam’iyya mu masu biyayya ne, a shirye muke a sake zama domin sasantawa,” in ji Shekarau.

Shekarau ya ce wannan dalili ya sa suka rubuta takarda suka aikawa shugaban jam’iyya, za kuma su bai wa ‘yan jarida da shafukan sada zumunta cewa abin da sukayi tsammani a yi ba shi aka yi ba

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...