Saurari premier Radio
23.9 C
Kano
Saturday, February 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAbdul attacker : Dan kwallon dake ceto Kano a kwallon kafa

Abdul attacker : Dan kwallon dake ceto Kano a kwallon kafa

Date:

Karibullahi Abdulhamid Namadobi

Fannin wasanni a jihar Kano na cikin wani yanayi da ke neman tallafi domin habbakashi, duk da yunkuri da hukumomi ke yi na yin hakan.

Jihar Kano ta tara yan wasa masu basira a fannin kwallon kafa da sauran wasanni.

Abdulmajid Aminu wanda akafi sani da Abdul attacker dan asalin jihar Kano ne a mai kimanin Shekarunsa 18, sai dai wani abin ban sha’awa shi ne yanda yake taka kwallo kamar yanda shahararrun yan wasan duniya ke yi.

PREMIER RADIO ta zakulo wannan matashi, kasancewar jihar ta tara zakakuran matasa, dubban daruruwa masu Basira a fanni daban daban na rayuwa.

Abdul attacker dai da ya fito daga dangin talakawa ‘cikin zakakuran ‘yan wasa a jihar Kano da tauraruwarsu ke haskawa a jefa kwallo.

Ya zuwa yanzu attacker ya zazzaga kwallaye 78 a tarihin rayuwarsa, cikin shekaru kadan da fara murza ledarsa a kungiyar a kwallon kafa ta Golden Bullet da Kuma Dabo Bebies dake a birnin Kano.

Daga cikin abinda ya kara haska wanann dan wasa shi ne yanda ya jefa kwallo 3 a ragar fitacciya kuma babbar kungiyar nan ta jihar Kano wato Kano Pillars, kungiyar da yanzu haka ke buga matakin gasar firimiya ta kasa (Nigerian Premier League).

Wannan yasa Kano Pillars gayyatar Abdul Attarker don murza leda a wasanninta na matakin share fage sabuwar kaka, kuma ya jefawa kungiyar kwallo guda a wasanni biyu da ya buga mata.

Yanzu haka Abdul attacker na taka leda a  cibiyar horas da ‘yan wasa mai suna Yaks Sports Limited dake jihar Lagos.

Cibiyar wasannin ta Yaks nayin wasanninta ne karkashin tsohon shahararran dan kwallon kafar Najeriya Mr Yakubu Ayegbeni.

Matashin Dan wasa Abdul yace a rayuwarsa  baya tsoron ratsa  yan wasan baya da zarar akwai yan wasa masu gara masa kwallo a fili yanda ya dace.

Bayanai sun hakkake Abdul dan wasan gaba ne dake zazzaga kwallo a raga komai rintsi, ya kuma ce yana son jefa kwallo ta kusuwar raga ko kuma ya yanke  yan wasan baya a guje kafin jefa kwallo.

“Daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa dake burgeni akwai shahararren dan wasan Najeriyar Yakubu Ayegbeni, Sai Zlatan Ibrahimovic da kuma Wayney Rooney Sai kuma Kareem Banzema”

“Abinda yafi bata min rai a kwallon kafa shi ne a tashi wasa ban jefa ‘ a raga ba, Haka kuma ina matukar kaunar tallafawa a wurin jefa kwallo a  raga” cewar a cewar Abdul Atterker

Da dama daga cikin Kungiyoyin kwallon kafar a Najeriya dai a yanzu sun zura idanu kan dan wasa Abdul kafin komawarsa cibiyar horas da yan wasa ta Yak Sports limited dake Lagos bayanda ya rattaba hannu.

Masu bibiyar kwallon kafa na hasashen cewa Abdul ka iya zamo dan wasan gaba a daya daga cikin kungiyoyin a nahiyar turai baya ga babbar tawagar super Eagles ta kasa Najeriya.

Kasantuwar iyayen Abdul masu karamin karfi amma hakan bai hanasu bashi dukkanin kwarin gwiwar da ta dace ba domin tabbatuwar da mafarkin sa ba a kwallon kafa.

Latest stories

Related stories