Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGurbataccen man da NNPC ta shigo da shi na sanadiyyar lalacewar motoci

Gurbataccen man da NNPC ta shigo da shi na sanadiyyar lalacewar motoci

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya tabbatar da cewa yana kokarin janye gurbataccen man fetur na kimanin Naira biliyan 16.5 da ya shigo da shi Najeriya.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa NNPC ta shigo da lita miliyan 100 na gurbataccen fetur mai dauke da sunadarin methanol fiye da kima —duk da cewa NNPC bai bayyana adadin man da ya shigo da shi ba.

Sanawarwar da Hukumar Mai na Kan Tudu (NMDPRA), wadda ke karkashin NNPC, ta tabbatar da shigo da gurbataccen man,

“Mun gano wani adadi na man fetur mai dauke da sunadarin methanol fiye da adadin da Najeriya ta kayyade da ke yawo a kasuwanni,”

ta kuma bayyana kokarin da NNPC ke yi na janye shi daga kasuwa.

A hirar da aka yi da shi a Sashen Hausa na BBC, Shugaban NMDPRA, Faruq Ahmed, ya ce, “Jiragen ruwa hudu na dakon man fetur ne aka shigo da su Najeriya, wadanda bayan shigowarsu muka gano man da suka kawo na dauke da sunadarin methanol fiye da kima.”

Ta ce, “Amma domin tabbatar da lafiyar ababen hawa da injina, an kebe  gurbataccen man da wuraren da ya shiga domin janye shi daga kasuwa da kuma motocin da suka fara dakon shi.”

NMDPRA ta bayyana cewa methanol sunadari ne da a koyaushe ake amfani da da shi wajen tace man fetur, kuma “An gano kamfanin da man ya shigo ta wurinsa, kuma NNPC da NMDPRA za su dauki matakan da suka dace na kasuwanci da sauransu da suka dace.

Wani bincike ya gano cewa wani kamfani daga kasashen Turai ne ya shigo da gurbataccen man Najeriya a madadin NNPC.

Kawo yanzu dai hukumar NNPC, wadda ita kadai ke shigo da tataccen mai Najeriya ba ta bayyana me ya faru har kamfanin ya shigo da gurbataccen man ba.

Janye gurbataccen man daga kasuwa

Faruq ya ce, bayan gano gurbataccen man, hukumar ta, “Dakatar da daukacin jiragen daga ci gaba da sauke man, muka kuma hana dafo-dafo da aka sauke man a Warri da Kalaba fitar da shi.

“Mun kuma yi nasarar dakatar da yawancin motocin da suka yi dakon wannan man, sai dai kuma wasunsu sun riga sun sauke a gidajen mai; Amma duk da haka, mun yi nasarar jenye man daga gidajen man.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa hukumar tare da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur na yin wani zama a Legas kan hanyoyin da za a tabbatar da samuwar wadataccen mai a fadin Najeriya.

Faruq Ahmed ya kara da cewa, “A yanzu haka mun kafa wani kwamiti mai wakilai daga NNPC, NMDPRA, manyan dillalan mai da dillalai masu zaman kansu, suna tattaunawa a Legas kan yadda za a janye gurbataccen man daga kasar nan, sannan a samar da mai kyan a kasuwanni.”

“Mun kuma gano kamfanin da ya shigo da man, ya sayar wa NNPC, kuma za mu dauki matakin shari’a a kan kamfanin. Abin da ya shafi kasuwanci kuma NNPC za da dauka.”

Babbar asara

’Yan kasuwa da masu lura da harkokin man fetur sun kiyasta cewa kudin gurbataccen man ya kai Naira biliyan 16.5.

Sun kuma bayyana cewa kawo yanzu wasu ababen hawa da suka yi amfani da gurbataccen man sun lalace.

Saboda gazawar NNPC wajen tace danyen mai, Najeriya kan fitar da danyen zuwa kasashen waje sannan ta shigo da tataccen domin amfani a cikin gida.

Wasu dillalan mai sun shaida wa manema labarai cewa tuni gurbataccen man ya fara yawo a wasu gidajen mai a Legal da Abuja da kuma jihohin Delta da Kuros Riba.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...