Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDokar kananan yara:Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani

Dokar kananan yara:Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Aƙalla mata 500 ne suka yi wani tattaki a Kano ranar Talata domin jan hankalin hukumomin  su gaggauta amincewa da dokar kare haƙƙin yara .

Matan sun yi tattakin ne ranar Talata a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar lauyoyi mata ta FIDA da suka gudanar, haka kuma wasu maza sun shiga su ma an yi tattakin da su.

An fara tattakin ne daga ofishin na FIDA a cikin birnin Kano zuwa gidan gwamnati domin kai kokensu da kuma miƙa buƙatarsu ta amincewa da dokar ba tare da ɓata lokaci ba.

Kano na cikin jihohi ƙalilan a Nijeriya da har yanzu ba su amince da wannan doka ba.

A baya-bayan nan jihar Kano ta auka cikin wani gagarumin juyayi bayan an zargi wani malami da sace ɗalibarsa ‘yar shekara biyar tare da hallaka ta.

Shugabar ƙungiyar ta FIDA Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman ta ce manufar tattakin shi ne su yi roƙo ga hukumomin Kano da masu faɗa a ji kan cin zarafin ƙananan yara da jan hankalinsu su lura cewa matsalar babbar masifa ce.

An shafe shekaru ana kira ga hukumomi a kasar nan da su sanya hannu a kuma fara aiki da dokar ta kare kananan yara.

Mafi yawan jihohin Najeriya a kudu da arewa sun amince da dokar, kuma tuni ta fara aiki a jihohin.

Barista Bilkisu ta ce amincewa da dokar da kuma fara aiki da ita zai taimaka sosai wajen magance matsalolin da yara ke fuskanta na cin zarafi da tozartawa.

Ta ce suna da kyakkyawan fatan cewa idan an amince da dokar to za ta taimakawa yara ta hanyoyi huɗu.\

Gata ga ƙananan yara

Babban gatan da dokar za ta yi wa ƙananan yara shi ne yi musu tanadin kyakkyawan yanayin tarbiyya tun ma gabanin a haife su. Ta ce dokar za ta tanadi cewa wajibi ne kafin a haifi yaro mahaifinsa ya zama yana da halin da zai iya rike shi.

Barista Bilkisu ta ce “dokar za ta yi tanadin cewa za a hukunta duk mahifin da aka samu yaronsa yana gararamba. Ta ce abin da ake so shi ne kowane yaro ya zauna a gaban mahaifinsa, ya kuma samu kulawar da ta kamata daidai gwargwadon halin iyayensa.

Ta ƙara da cewa a kan samu lokuta da dama da iyaye maza su kan gudu su bar iyaye mata da ɗawainiyar yara, kamar yadda ta ce ta taɓa faruwa wani uba ya gudu ya bar matarsa da ƴaƴa biyar.

Matakan tarbiyya

Dokar ta kare ƙananan yara ta kuma tanadi yadda za a yi wa yara tarbiyya da matakan da za a bi wajen tarbiyyar yaran.

Barista Bilkisu ta ce dokar ta yi tanadin yadda za a ci gaba da tarbiyyar yara idan mahaifinsa ya mutu ko kuma aka samu rabuwar aure, ta yadda yara ba za su tagayyara ba.

Samar da lauyoyi ga yara da aka ci wa zarafi

A tanade-tanaden dokar ta kare ƙananan yara, akwai hanyoyi masu sauƙi da za a bi domin samarwa da ƙananan yara lauyoyi a duk lokacin da aka ci zarfinsu.

Ta kuma ce za a samar da hanyoyi masu sauƙi da za a tabbatarwa da masu laifi laifinsu saɓanin yadda lamarin ya ke da wahala a yanzu.

Haka za a sauƙaƙa matakan shari’a ta yadda za a tabbatar da cewa an hukunta mai laifi domin ya zama darasi ga wasu.

Kawo ƙarshen tallace-tallacen yara

Wani gata da dokar za ta yi wa ƙananan yara shi ne hana tallace-tallacen ƙananan yara da gararambar yara sasakai.

Haka kuma dokar za ta tanadi hukunci kan duk iyayen da aka samu da laifin sakin yaransu suna tallace-tallace a kan tituna.

Barista Bilkisu ta ce a yanzu rayuwar ƙananan yara suna cikin halin tsaka mai wuya sakamakon cin zarafin da suke fuskanta a yayin tallace-tallace da gararamba.

Batun dokar ta ƙananan yara dai ta jima tana sanya fargaba a zukataun jama’a da dama musamman a arewacin Najeriya.

Malaman addinin sun sha nuna shakku kan dokar da kuma suka kan tanade-tanaden dokar ta asali da Najeriya ta amincewa da ita a matakin gwamnatin tarayya.

Wasu dai na ganin cewa idan aka amince da dokar to za ta lalata tarbiyyar yara, musamman a yankunan da addinin ke tasiri wajen yadda ake tarbiyya.

To amma Barista Bilkisu ta ce sam babu wani abin fargaba, domin kowace jiha tana da damar ta daidaita dokar da al’adunta da kuma addinin mutanenta.

Ta ce gabanin dokar ya kamata hukumomi su ji ta bakin jama’a ta kuma yi la’akari da ra’ayoyinsu wajen tasara dokar da amincewa da ita da kuma fara aiki da ita.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories