Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin Kanywood: ‘Yan fim din Hausa azzalumai ne-Sarkin waka

Rikicin Kanywood: ‘Yan fim din Hausa azzalumai ne-Sarkin waka

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen mawakin nan Naziru M Ahmad, (Sarkin Waka) ya ce galibin masu shirya fina-finan  Hausa azzalumai ne da ke tauye hakkin wadanda ke aiki a karshinsu.

Naziru ya bayyana hakan ne ta cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa mai mintuna shida ranar Alhamis yana kalubalantar ‘yan fim din Hausa.

Idan za iya tunawa dattijiwa Ladin Cima a wata hira da ta yi da sashin Hausa na BBC ta bayyana yadda ake bata N2000 idan ta yi fim.

Wannan dai ya harzuka masu shirya fina-finai kamar su Ali Nuhu da Falalu Dorayi, suka fito suna caccakar wanna tsohouwa.

Sai dai Naziru Sarkin Waka ya baiwa wanna tshohuwa kariya inda ya bayyana irin cin zalin da ‘yan fim din ke yiwa wadanda ake sakawa a fim.

Ya ce ko kadan babu karya a cikin kalaman dattijuwar kuma bai kamata a fito a yi mata irin wannan cin zarafi ba,

“Na taba Kiran wata dattijuwa Aikin fim Bayan ta gama na dauki kudi na bata kawai sai matar nan ta rikice tana yimin godiya kamar ta yimin sujjada , sai na tambaya ya haka sai aka ce ai dubu biyu Dubu uku ake basu, yau kuma ta ji Dubu 10 a hannunta shi yasa ta rikice”. Inii Nazir m Ahmad

Wasu ma sai anyi lalata da su

Sarkin Waka ya ce wasu matan ma sai anyi lalata da su sanan ake sanyasu a cikin fim, yayin da wasu ma su ke biyan kudin dan sanya su.

“Duk da bana harkar fim sosai amma nasan  maganar Ladin Cima gaskiya ce, sannan muna sane da yadda wasu ma maimakon a biyasu idan an saka su a fim sai dai su su biya.

“Wasu kuma yan matan ayi lalata dasu kafin a saka su a fim, wannan Kowa ya sani”. Inji Sarkin waka

Naziru ya kara da cewa masana’antar tana samun nakasu, kuma ya kalubalanci duk wadanda suka karyata zancen dattijuwar da cewar su yi rantsuwa kan abunda da ta fada ba gaskiya ba ne.

Ali Nuhu da Falalu suna boye gaskiya

Naziru ya kalubalanci Ali Nuhu da Falalu A Dorayi bisa take gaskiya kan furucin su, inda ya ce ya kalubalance su su fito su musanta zancensa idan ba gaskiya ya fadaba.

Sai dai shi ma a safiyar  Juma’ar nan mai Shirya fina-finan Hausa nan Abubakar Bashir Mai shadda ya mayar masa da martani tare da Karyata dukkanin kalaman Nazirun.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...