Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiExecutive order no 10: Me dokar ta ke nufi

Executive order no 10: Me dokar ta ke nufi

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kotun Ƙolin kasar nan  ta yi watsi da doka mai lamba goma wadda aka fi sani da “Presidential Executive Order No. 00-10 of 2020”.

Dokar dai ta bayar da umarni ga babban akanta janar na kasa ya cire kuɗaɗe kai tsaye daga alawus-alawus na jihohi domin bai wa ɓangarorin shari’a na jihohi.

Alƙalan Kotun Ƙolin  waɗanda suka yi zama a ranar Juma’a sun amince da cewa dokar da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ta saɓa ƙa’idar kundin tsarin mulki.

A bara ne babban lauyan gwamnatin kasa ya shigar da ƙara a gaban Kotun Ƙolin domin ƙalubalantar halarcin dokar mai lamba goma wadda gwamnatin ta yi a bara domin ta sakar wa ɓangarorin shari’a da ma’aikatan majalisu na jihohi mara su samu kuɗinsu kai tsaye daga tarayya.

Alƙalan kotun sun ce dokar mai lamba goma ta bayyana  cewa ta saɓa doka ta hanyar cin karo da sashe na shida da takwas uku cikin baka na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya bai wa gwamnatin tarayyya damar bai wa kotunan jihohi da na shari’a da na ɗaukaka ƙara da na gargajiya kuɗi.

Haka kuma alƙalan Kotun Ƙolin shida sun amince da hukuncin sauran alƙalan inda suka ce da gaske gwamnatin tarayya ba ta da ikon bayar da irin wannan doka.

Haka kuma jihohin ƙasar nan sun kai kuka ga alƙalan kotun inda suka ce suna amfani da kuɗaɗen su wajen gudanar da manyan ayyukan kotun tun daga 2009 inda suke so gwamnatin tarayya ta mayar musu da kuɗinsu.

Kan wannan batu, alƙalan Kotun Ƙolin huɗu suka ce gwamnatin tarayya ba za ta biya ko sisi ba haka kuma gwamnatin jihohin za su ci gaba da bayar da kuɗaɗe ga kotunan da ke jihohin.

Menene dokar ta ƙunsa?

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a doka mai lamba goma a ranar 22 ga watan Mayun 2022 domin sakar wa ɓangaren shari’a da majalisu na jihohin kasar nan 36 mara su samu kuɗaɗe.

Dokar na nufin babban akanta janar na kasa na da damar cire kuɗin jihohi domin bai wa majalisu da kuma ɓangarorin shari’a na jihohi.

A lokacin da shugaban ya sanar da saka hannu kan dokar a shafin Twitter a lokacin, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta domin ƙara inganta ayyukan gwamnati.

Shugaban ya ce ya yi dokar ne bisa ƙarfin da sashe na biyar na kundin tsarin mulki na 1999 ya bashi.

Wannan na nufin kuɗin da gwamnatin tarayya ke bai wa ɓangarorin shari’a na jihohi da majalisu ba zai ci gaba da kasancewa a hannun gwamnoni ba.

Hakan ne ya sa jihohi 36 na kasar nan suka fusata har manyan lauyoyinsu suka shigar da ƙara a ranar 17 ga watan Satumban 2020 domin ƙalubalantar lamarin

Latest stories

Related stories