Ronaldo ya bayyana matuƙar girmamawarsa ga Messi, yana mai bayyana cewa irin gudunmawar da ɗan wasan ya bayar ga ƙwallon ƙafa ta cancanci yabo, Messi wanda ya shafe shekaru yana jagorantar tawagar Argentina, ya lashe manyan kofuna da dama ciki har da Copa América da kuma gasar cin kofin duniya ta 2022.
Ronaldo da Messi sun shafe sama da shekaru goma suna fafatawa a matsayin manyan taurarin ƙwallon ƙafa, musamman a lokacin da Ronaldo ke taka leda a Real Madrid, Messi kuma a Barcelona.
Bankwanan Messi da tawagar Argentina ya sake jawo hankalin duniya kan tarihin fafatawar manyan ‘yan wasan biyu, waɗanda suka yi tasiri sosai a tarihin ƙwallon ƙafa.
