Wani matashin mawaki daga jihar Kano, Khalid Umar, wanda aka fi sani da Capital K, ya rera wata waka mai taken We Want Peace da harsuna 11, domin isar da sakon zaman lafiya ga duniya.
Mawakin ya ce ya shirya wakar ne bisa la’akari da rikice-rikice da tashe-tashen hankula da ke addabar kasashe daban-daban, ciki har da Najeriya, Rasha, Iran da Amurka.
Capital K, wanda ya fara harkar waka a shekarar 2018, ya bayyana cewa yana fatan wakar za ta isa ga mutane a sassan duniya, tare da jan hankalin shugabannin kasashe su rungumi zaman lafiya.
Ya ce ya yi amfani da harsuna 11 da suka hada da Turanci, Swahili, Larabci, Italiyanci, Farisanci, Hindi, Ibrananci, Sifaniyanci, Faransanci, Rashanci da Ukrainiya, domin tabbatar da cewa sakon ya isa ga al’ummomi masu bambancin harshe da al’adu.
Mawakin ya kara da cewa ba wai ya hada harsunan ne don nuna bambancinsu kawai ba, illa domin isar da sako guda daya, wato bukatar zaman lafiya a duniya.
Ya kuma bayyana cewa yana iya magana da wasu daga cikin harsunan da ya yi amfani da su, ciki har da Turanci, Faransanci, Sifaniyanci, Larabci da Hindi, yayin da yake ci gaba da koyon wasu.

Capital K ya ce yana da yakinin cewa baiwar da Allah ya ba shi a fannin waka za ta taimaka masa wajen cimma burinsa na daukaka sunan Najeriya a duniya.
Mawakin ya bayyana cewa yana shirin fitar da wakar We Want Peace a dandalin Audiomack, domin samun damar isar da sakon ga dimbin masu sauraro.
ya ce yana da yakinin cewa baiwar da Allah ya ba shi a fannin waka za ta taimaka masa wajen cimma burinsa na daukaka sunan Najeriya a duniya.