A yau Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, ne za a bayyana wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana, a wani biki da za a gudanar a birnin London na ƙasar Birtaniya.
Daga cikin ’yan wasan da ake ta hasashen za su iya lashe babbar kyautar akwai kyaftin ɗin Ingila kuma ɗan wasan Bayern Munich, Harry Kane, da matashin tauraron Barcelona na Sifaniya, Lamine Yamal, da kuma Kylian Mbappé na Real Madrid.
Rahotannin masu sharhi kan ƙwallon ƙafa sun nuna cewa Harry Kane na samun goyon baya sosai a hasashen masu yin fare, yayin da Lamine Yamal da Mbappé ke cikin fitattun ’yan takarar.
Za a gudanar da bikin ne a London Palladium, inda za a karrama fitattun ’yan wasan ƙwallon ƙafa na duniya bisa bajintar da suka nuna.
Bikin na bana ya zo daidai da cika shekaru 70 da fara bayar da kyautar Ballon d’Or a shekarar 1956.
A ganinku, tsakanin Harry Kane, Lamine Yamal da Kylian Mbappé, wa ya fi cancantar lashe kyautar Ballon d’Or ta 2026?
