Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeAl'aduMasarautar Kano: Dalilin nadin Hakimai 6 | Premier Radio | 28.04.2023

Masarautar Kano: Dalilin nadin Hakimai 6 | Premier Radio | 28.04.2023

Date:

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, Ya nada sababbin Hakimai guda shida.

Da yake jawabi lokacin nadin, Sarkin yace an yi hakan ne bisa cancantarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Wadanda aka nada Sarautun sun hadar da Alhaji Abbas Maje Ado Bayero a Matsayin Bauran Kano da Alhaji Kabiru Ado Bayero a Matsayin San Turakin Kano da Alhaji Umar Ado Bayero wanda aka nada shi Yariman Kano.

Sauran sune Alhaji Tijjani Ado Bayero a Matsayin Zannan Kano da Alhaji Auwalu Ado Bayero a Matsayin Sadaukin Kano da Alhaji Ado Ado Bayero a Matsayin Cigarin Kano.

Mai martaba Sarkin Kano ya horesu da su sanya halayyar magabatansu na yin koyi da kyawawan halaye wadanda suka hadar da juriya da hakuri da amana da tausayawa talakawa.

Yace su dauki halayyar magabata ta mika dukkan al’amuransu ga Allah tare da yin biyayya ga wadanda suka tarar a cikin tsarin hakimci da kuma yin da’a kamar yadda suka taso sukaga anayi Kasancewarsu dukkanninsu yan gidan sarautar Kano ne.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakiman da aka nada su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tareda gudanar da aikinsu da gaskiya da amana tareda Sanya tsoron Allah.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories