Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Gwamnatoci...

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Gwamnatoci da Mawadata su fito su tallafawa marasa karfi a cikin al’uma

Date:

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Gwamnatoci da Mawadata su fito su tallafawa marasa karfi a cikin al’uma.

Sarkin yayi wannan kira ne a wata hira da yayi da yan jaridu a fadarsa dangane da bikin ranar Agaji ta duniya.

Yace a matsayinsu na Shugabani kuma wadanda suke tare da talawa kuma suke sauraron koke kokensu a kullum ya zama wajibi su kara jan hankalin wadanda suke da wadata su dinga tallafawa makontansu wadanda basu dashi.
Sorkin

A gefe guda kuwa sarkin yayi bayanin cewa koda a kwanankin baya ya bayyanawa shugaban kasa halin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa a wani zana da shugaban kasar yayi da Sarakunan kasar nan.

A bangaren hidintawa ga kungiyar agaji kuwa Sarkin yace kimanin shekaru talatin (30) kenan yana bayar da gudunmawa a kungiyar Agaji ta Jama’atu Nasrul Islam ta kasa.

Alhaji Aminu ado Bayero yace ya zagaya dukkanin lungu da Sako na kasar nan domin gudanar da aikin hidamtawa al’umma a kungiyar bayar da agaji ta Jama’atu Nasrul Islam a matsayinsa na shugaba.

mai martaba sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero yayi bayanin cewar kungiyar bayar da Agajin ta samo asali ne tun zamanin Annabi Muhammad SAW,
Inda ya bayyana agaji da cewar tushensa shine addinin musulunci

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...