Majalisar Dattawan ƙasar nan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi nazari kan yiwuwar dakatar da yaƙin neman zaɓen shekarar 2027 a wasu jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro.
Ƙudurin ya fito ne daga Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmad Ningi, a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis, inda ya ce akwai buƙatar a duba yanayin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a ƙasar nan.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Sanata Ningi ya bayyana cewa bai dace ƴan majalisar su yi watsi da halin da ake ciki a wasu yankuna ba, musamman ganin cewa su na gudanar da aikinsu ne cikin kwanciyar hankali a birnin tarayya, Abuja.
Ya ce dakatar da duk wasu tarukan siyasa a yankunan da ke fama da rikice-rikicen tsaro na daga cikin matakan da ya kamata a ɗauka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sanatan ya lissafo jihohin da matsalar tsaro ta fi ƙamari da suka haɗa da Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi, da kuma wasu sassan jihar Kano.
Gargaɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ciki har da kai hare-hare kan sansanonin soji da kuma sace mutane domin neman kuɗin fansa.
