Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Ahmad Nasir El-Rufai, a gaban mai shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja.
Ana tuhumar El-Rufai ne da zargin hannu a tatsar bayanai daga wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
A cewar DSS, ana zargin tsohon gwamnan da yin kutse cikin wayar Ribadu, abin da ya saɓa wa sashe na 7 (b) da (c) na kundin kare bayanan ƙasa masu muhimmanci na 2024, da kuma sashe 5(1) na dokar hana aikata laifuka ta intanet ta 2024 da aka yi wa gyaran fuska.
Sai dai El-Rufai ya musanta zarge-zargen da ake yi masa.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Oluwole Aladedoye (SAN), ya roƙi kotu da ta ba su kwanaki uku domin sauraron shari’ar.
Bayan kammala sauraron jawabai daga lauyoyin ɓangarorin biyu, mai shari’a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron shari’ar zuwa ranakun 18, 19 da 20 ga watan Mayu domin ci gaba da shari’ar.
