Ƙungiyar Dattawan Kiristoci ta Ƙasa, NCEF, ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta danganta matsayinta da abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Tinubu wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arzikin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da shugabanta, Dr. Samuel Danjuma Gani, ya sanya wa hannu a ƙarshen mako, NCEF ta ce ana jagorantar ƙasar ta hanyar da ke haifar da ƙarin fargaba maimakon fata.
Ƙungiyar ta ce maimakon Shugaba Tinubu ya nemi wa’adi na biyu, ya kamata ya mayar da sauran lokacin mulkinsa wajen sake fasalin Nijeriya da kuma samar da sabon Kundin Tsarin Mulki.
Dattawan Kiristocin sun kuma yi kira ga ƙabilu daban-daban, ƙungiyoyin al’adu da sauran masu ruwa da tsaki da su fara shirye-shiryen ganin an amince da sabon Kundin Tsarin Mulki kafin babban zaɓen 2027.
Sun kuma yi gargaɗin cewa kada a ɗauki haƙurin ’yan Nijeriya da wasa, suna mai cewa al’umma na matuƙar ɗokin ganin sauyi a ƙasar.
