Gwamnatin Jihar Lagos ta ce jami’an tsaro sun kama mutane 27 da ake zargi da lalata wasu sassan sabuwar gadar da ta haɗa Festac Town da Alakija.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya ce an kama mutanen ne yayin wani samamen dare da jami’an Rapid Response Squad da Kick Against Indiscipline suka gudanar.
Ya ce jami’an sun gano ana cire sandunan ƙarfe, kayan ƙarfafa ginin gada, igiyoyi da sauran muhimman kayan gini daga ƙarƙashin gadar.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa irin wannan aika-aika na iya jefa rayuwar masu amfani da gadar cikin haɗari, tare da haddasa asarar makudan kuɗaɗen da aka kashe wajen gina ababen more rayuwa.
Ta ce za a gurfanar da mutanen da aka kama a gaban kotu bisa dokokin jihar, yayin da jami’an tsaro za su ci gaba da kai samame domin dakile lalata kadarorin gwamnati.
